ABIN TAUSAYI: Ta Yi Ta Yawon Neman Mai P.O.S Din Da Yake Da Kudi Domin Ta Cire Kudin Da Za Ta Sayi Jinin Da Za A Karawa Danta A Asibiti

ABIN TAUSAYI: Ta Yi Ta Yawon Neman Mai P.O.S Din Da Yake Da Kudi Domin Ta Cire Kudin Da Za Ta Sayi Jinin Da Za A Karawa Danta A Asibiti.
Wani abin tausayi da ya auku a yammacin yau Talata a garin Mararrabar Abuja da jihar Nasarawa shine, yadda wata mata ta yi ta yawon neman mai p.o.s din da za ta ciri kudi domin ta biya kudin da a siyawa danta jinin da za a kara masa a asibiti.

Da kyar dai matar ta samu wani mai p.o.s da yake da dan kudin da bai wuce mutum daya ya karbe ba, inda da kyar ya ba ta naira dubu goma a ciki, wanda shi ma sai da ta biya dari biya kafin ya ba ta.

Matar ta ce ta dauki tsawon awanni tana neman wurin da za ta cire kudin duk da cewa dan nata yana cikin yanayi na rashin lafiya.

Wani abin mamaki shine, yawancin masu harkar p.o.s a garin na Mararraba idan mutum zai cire kudi ba sa ba shi kasa da naira dubu uku ko biyu, saboda karancin kudi. Domin a cewar su su ma da kyar suke samo kudin a banki.

Kusan dai yanzu samun kudi a ATM sai mai rabo saboda karancin kudi.
Previous Post Next Post