KALLI YADDA AKA KAIWA MATAR GWAMNA FINTIRI HARI A MUBI

An kaiwa tawagar ayarin motocin matar Gwamna Fintiri hari a Mubi

Wasu da ba'a san ko su wanene ba sun kaiwa tawagar ayarin motocin uwargidan Gwamnan jihar Adamawa Hajiya Lami Ahmadu Fintiri hari a kauyen muchalla da ke karamar hukumar Mubi ta Arewa a Jihar Adamawa.

Wakilin Yola 24 ya ruwaito cewa Maharan sun yi nasarar lalata motoci biyar, da suka hada da Bus Bus, da Motar gaggawa motar manema labarai da dai sauransu.
Matar Gwamna Hajiya Lami ta yi kira ga matasa da cewa kada su bari duk wadannan ’yan siyasa marasa kishin kasa su yi amfani da su, wadanda ba su da wani abin da za su ba su sai dai sanya su cikin rikicin siyasa.

Previous Post Next Post