RA'AYI: Abinda Baku Sani Ba Game Da Atiku Abubakar
Daga Babangida Isa
A dukkan lokacin da aka yi maganar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyar PDP wasu magoya bayansa suna jingina shi da mai kishin addinin Muslunci don samar masa da farin jini ta karfi bayan ba sa iya gaya wa jama'a abinda suka ɓoye game da shi Atiku Abubakar ɗin.
Shekarar da ta gabata wata ɗaliba a jami'ar tarayya dake jihar Sokoto ta soki janabin Manzon Allah (SAW) inda al'ummar musulmi suka nuna ɓacin ransu akai, inda Atiku Abubakar ɗin ya fito ya nuna rashin jin dadinsa kan kashe ta da aka yi.
Yayin da ya fuskacin turjiya daga jama'a nan take saboda yana tsoran rasa ƙuri'arsa ya fito ya ce ba shi ya yi ba, shin wanda bai isa da shafukan sada zumuntansa ba ne zai iya kula da shugabancin Najeriya?
Farfagandar da ake yaɗawa da sunan Atiku mai kishin musulunci ne, lokaci yayi da yakamata al'umma su gane manufa ce ta siyasa tare da neman ƙuri'a kawai.