Ra'ayi Riga...Masu salon magana kan ce rana ba ta karya sai dai uwar diya ta ji kunya,

Ra'ayi Riga...

Masu salon magana kan ce rana ba ta karya sai dai uwar diya ta ji kunya, ranar Asabar din nan ne miliyoyin 'yan Najeriya suka shirya fita don zabar sabon shugaban kasa da kuma 'yan majalisar dattijai da na wakilai.
To shin menene muhimmancin fita don kada kuri'ar?, wanne irin shiri kuka yi don yin zaben ?

Wasu daga cikin batutuwan da muke fatan dubawa kenan a filin na mu na Ra'ayi Riga na wannan makon wanda Imam Saleh zai tsara.
Previous Post Next Post