Soyayyar Da Al'ummar Jihar Bauchi Ke Yi Wa Buhari Ta Rikide Ta Koma Kan Atiku.

Soyayyar Da Al'ummar Jihar Bauchi Ke Yi Wa Buhari Ta Rikide Ta Koma Kan Atiku 

A yau Talata Mai Girma Wazirin Adamawa Alhaji Atiku Abubakar, ya kaddamar da yakin neman zabenshi a jihar Bauchi.

Dubunnan mutane daga Birni da kauye ne suka fito suka tarbe shi a lokacin da ya ziyarci jihar. 
Hakika al-ummar jihar Bauchi sun nunawa Mai girma Wazirin Adamawa Alhaji Atiku Abubakar, tsantsar soyayya da kauna kamar yadda suke nuna Buhari a shekarun baya. 

Duk wasu nasarori da ake bukata a zabe mai zuwa Atiku Abubakar ya riga da ya same su. 

Muna fatan Insha'Allah Atiku Abubakar ya zama Alkhairi ga al-ummar Najeriya baki daya.
Previous Post Next Post