Yan Bindiga Kun Shiga Uku Idan Na Zama Shugaban Kasa, Cewar Tinubu

'Yan Bindiga Kun Shiga Uku Idan Na Zama Shugaban Kasa, Cewar Tinubu

...Ba zan zuba Ido irin haka yana faruwa a mulkina ba, cewar Asiwaju.

...Hakki ne akan gwamnati ta kare lafiya da dukiyar kowane ɗan Nijeriya, Inji Tinubu.
Ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya bada kyautar Naira Miliyan 100 ga iyalai da yan uwan mutanen da harin yan bindiga ya hallaka a ƙaramar hukumar Bakorin jihar Katsina.

Da yake nuna alhini da ta'aziyar ga mamatan, Tinubu ya bayyana baƙin cikinsa da kuma ɓacin rai game da lamarin, inda ya bada tabbacin cewar ba zai bar irin wannan aika-aika ya cigaba da gudana ba muddin ya zama shugaban kasar Najeriya a zaɓen 2023.

Tinubu yace "Ba zan zuba Ido irin haka yana faruwa a Mulki na ba, hakkine akan gwamnati ta kare lafiya da dukiyar kowane ɗan Najeriya.
أحدث أقدم