SIYASAR KANO: Limaman Juma’a A Jihar Kanò Sun Yí Huduba Kan Muhimmancin Zaben Dr. Nasiru Yusuf Gawuna

SIYASAR KANO: Limaman Juma’a A Jihar Kanò Sun Yí Huduba Kan Muhimmancin Zaben Dr. Nasiru Yusuf Gawuna 

A wannan rana ta Juma'a limamai da dama a masallatan Juma'a sun gabatar da huɗubobi akan muhimmancin zaɓen ɗan takarar gwamnan Jahar Kano na jam'iyyar APC, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna.


Shaíkh Sayyadi Hussan da ke zaman babban limamin masallacin Juma'ar Daruln Haq, ya faɗa cewa "Gawuna ɗan siyasa ne wanda ya sha bamban da saura, bai taɓa faɗa da malaman addini ba, bai taɓa hawa mumbarin siyasa ya yi katobarar da ta nuna ba shi da ilimin addini ba. Kalamansa cike su ke da ƙanƙan da kai da bar wa Allah ikonsa kan komai. Wannan mutum ya cancanta mu zaɓe shi".

Shi ma ta cikin tasa huɗubar, Liman Zailani Sallau na masallacin Ummul Huda, ya yi bayani cewa "salihanci da kamun kai na Dr. Gawuna kyawawan ɗabi'u ne waɗanda musulunci ya tanadar. Mutum wanda ya siffanta da su abin so ne ya zama shugaba".

"Ina mai yi muku masiha akan zaɓen Gawuna ranar zaɓe a matsayin gwamnan Jahar Kano. Na faɗa yanzu akan mumbarin kowane musulmi mai kishi ya ji domin a fita a yi wa musulunci hidima domin kanmu za mu amfanar duba da yadda Gawuna ke ƙaunar addini da son al'umma. Inji Shaíkh Nur, masallacin Darul Qira'at.

✍️ Aliyu Umar Gama
Previous Post Next Post