BADAKALAR CANJIN KUDI: Tambayoyi Ga Malam Nasir El-Rufai .

BADAKALAR CANJIN KUDI: Tambayoyi Ga Malam Nasir El-Rufai 

Daga Hon Biniya Yahuza Gabari

Mun wayi gari cike da mamaki ganin yadda ka dage akan wannan canjin kudi da sunan nema wa talaka sauki. Abin tambaya anan shine, wani talakan kake nufi, wanda baka san yana wahala ba sai yanzu da akayi abinda ya shafe ka kai tsaye?
Kana nufin tun 2015 talaka bai taba shiga damuwa ba sai yanzu? 

Idan don talaka kake wannan abu;
1. Meyasa baka kai karan gwamnatin tarraya akan matsalar rashi tsaro daya addabi arewa (ciki harda Kaduna) ba? Ko ba talaka ake kashewa ba? 

2. Mene yasa baka kaisu kara akan kidnapping da mukayi ta fana dashi a hanyoyi da garuruwan jihar Kaduna ba? 

3. Meyasa duk wahalan man fetur da talaka keyi baka kai kara ba?

4. Mene yasa ka rushe ma talakawa shagunan ka sayar wa masu kudi yan'uwanka? 

5. Mene yasa ka hana talakawa cinikayya a kan tituna domin neman abinci? 

6. Mene yasa ka kori talakawa da hannunka daga ayyukan gwamnati mabambanta? 

7. Mene yasa ka rushe ma talakawa muhalli ba tare da rage masu radadi ba?

8. Mene yasa baka kai kara lokacin da ASUU suka tafi yajin aiki har na tsawon watanni 6 ba?

9.Mene yasa ka kara kudin makaranta a KASU

10. Mene ya sa yaran Talakawa (yaran makaranta Asu) suka yi wata 9 a gida baka kai karar gwamnati ba.

Wanda ya'yan talakawan jihar Kaduna ke samun saukin karatu?

Ko kana nufin canjin kudi yafi duk wadannan shafan talaka?

A karshe muna rokonka, Don Allah idan har domin talaka kakeyi, ka janye wannan karan har sai bayan an gama zabubbuka (Na Shugaban Kasa da na Gwamnono) sai ka shigar.
Previous Post Next Post