Ba Don Talakawa Gwamnonin APC Suke Adawa Da Canjin Kuɗi Ba, Inji Naziru Sarkin Waƙa.

Ba Don Talakawa Gwamnonin APC Suke Adawa Da Canjin Kuɗi Ba, Inji Naziru Sarkin Waƙa.


Fitaccen mawaƙin nan Naziru M. Ahmad wanda ake yi wa laƙabi da Sarkin Waƙa ya bayyana cewa "yanzu har akwai wani Gwamna wanda zai ce maka sai yanzu ne yake jin tausayin taalaka?

Lokacin farkon mulkinsu wanne irin abu ne ba su yi wa talaka ba, an yi lokacin korona, babu malamin da ba iyi kira akan su sassautawa talaka ba, idan an ba su abinci da kuɗi a lokacin korona ɓoyewa suke, duk a wannan lokacin ba su ji tausayin talaka ba, an kashe mutane duk ba su je gurin shugaba Buhari ba sai yanzu? 

Ba bukatar talaka ce ta kai su ba, matsalar su ce ta zaɓe, wanda a tunanin su idan an ɗaga za su ci zaɓe. Inji Naziru Sarkin Waƙa.
Previous Post Next Post