CANJI KUDI: Muhimmin Sako Zuwa Ga 'Yan Nijeriya...Wasu daga cikin abubuwan da yakamata 'yan Najeriya su fahimta dasu.

CANJI KUDI: Muhimmin Sako Zuwa Ga 'Yan Nijeriya

...Wasu daga cikin abubuwan da yakamata 'yan Najeriya su fahimta dasu.
Daga Real Buroshi Mawaka Sokoto

Ana kashe mutanen mu na Ƙauye da Birnin da dama a Nijeriya musamman 'yan Arewa wanda har yanzu ana kan zubar da jinin 'yan uwanmu, amma gwamnoni su kayi gumm da bakinsu su kayi shuru Kamar basa nunfashi har zuwa yanzu babu magana mai daɗi daga garesu.

An shiga yajin aikin ASUU wanda yazamo silar illata rayuwar karatun 'ya'yan talaka, amma gwamnoni su ka kasa tada jijiyoyin wuya akan su goya mana baya, na ganin karshen wannan strike sai su ka raba ƙafa ( su dai ba su ce adaina ba kuma basu ce a cigaba ba) bayan 'ya'yan su na kasashen waje suna dawowa da digiri a daidai lokacin da mu ke fuskanta yajin aiki a kasar.

Anyi wata 5 biyar ana fama da matsalolin man Fetur amma gwamnoni ba su je fadar shugaban kasa su ka ce ga hanyar da za'a bi takala yaji saukin walwala ba, haka ma su kayi Kwanciyar su a gidajen su na kallon BBC da Aljazeerah sai faman kwasar dariyar talaka su ke Yana shan wahala.

Sai a yanzu wannan yanayin Canjin kuɗi sun zo su na tada jijiyoyin wuya da tada hankali da barazana akan waɗanda su ke da hannu wajen canja fasalin kuɗin, inda su ke jadadda goyon bayan su ɗari bisa ɗari na damuwar su, domin zaɓen da ke gabato musu ne zai iya samun tangarɗa idan har ba suyi barazara ga wannan al'amarin ba.

Da haka nake Kira zuwa ga al'ummar Najeriya cewa su Yi ɗamara su zare dantse ga duk gwamnan da yake Sintiri wajen sukar wannan al'amarin zuwa haujin zaɓe, da su ɗaukar masa matakin gaggawar kifar da gwamnatin sa da yaran siyasar sa a kowacce irin jam'iya yake don ba ƙaunar mu yake ba yana Yi ne akan mafitar ta zaɓe, domin yin hakan shine mafita agurin mu 'yan arewa.

Daga karshe ina kara Kira da tunatarwa ga 'yan uwana 'yan Najeriya musamman 'yan arewancin najeriya cewa Su ɗauke wannan al'amarin a matsayin abunda Allah S.W.T yazo dashi wanda muke Kyautata zaton gyara ne garemu talakawa, sannan mu rungume Qaddarorin da Allah ya jarabemu dasu waɗanda su ka zo da waɗanda su ke Shirin zuwa, domin Allah S.W.T ba shi halacci cuta ba saidai yayi maganin ta, haka ma duk inda wahala ta ke daɗi yana nan zuwa bayanta.
أحدث أقدم