Sai Talaka Ya Siyar Da Kwanon Masara Hudu Sannan Zai Iya Siyan Ledan Maggi Guda Daya
Tabbas wallahi talakawa zasu kara talaucewa masu kudi kuma zasu sake tara arziki domin sune masu kamfanoni kuma sune diloli masu siyarwa talakawa kuma duk duk sune masu karawa kaya kudi.
Domin wallahi wannan karyewar kayan masarufin da sauran kayayyakin akan talakawa zai kare.
Wallahi muna fata kuma muna son kowane irin kaya yayi arha tun daga kan na kamfanoni, kayan masarufi da sauran kayayyakin komai yayi arha, amma bamu son iya kayayyakin talakawa ne kadai zai karye.
A yanzu haka wasu wuraren ana saida buhun masara dubu 13 karamin kwano 170, sai talaka ya saida kwanan masara Hudu kafun ya sayi ledar Maggi guda daya tak.
Matukar iya kayayyakin talakawa ne da suke dan saidawa wasu a shaguna wasu a kauyuka wasu a cikin gidajensu suka karye suka tafka asara na tabbata talakawa da dama zasu kara talaucewa fiye da yadda ake a yanzu.
Wallahi duk wanda ya kasa kayanshi a kasuwa babu masu siya kuma baida kudin Cefane dole ya karyar da kayan ya siyar asara domin ya samu kudin da zai kai gida a yi amfani dasu. Da yawan mutane jarinsu zai karye a wannan lokacin matukar ba'a samu chanji ba.
Masu dariya su cigaba da yi amma su sani ko a shekarun baya talaka bashi yake kara kudin kaya ba.
Allah ya kawo mana karshen wannan musifan.