PDP PCC: Atiku Ya Yi Alƙawarin Sakin Shugaban Kungiyar 'Yan Tawayen Biyafara (IPOB) Nnamdi Kanu Ba Tare Da Shari'a Ko Sharaɗi Ba Idan Ya Zama Shugaban Kasa
•-Ɗan takarar shugaban ƙasar na PDP ya ce zai yi duk mai yiwuwa don ganin ya dawo da zaman lafiya a yankin Kudu na Inyamurai.
Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben watan Fabrairu, Atiku Abubakar, a jiya ya bayyana kudirin lallai zai saki shugaban kungiyar yan taada na Inyamuran Biyafara (IPOB), Nnamdi Kanu, ba tare da shariah ko sharadi ba idan ya zama Shugaban Najeriya.
Tun a watan Yunin 2021 ne Kanu ke tsare a hannun hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) lokacin da gwamnatin tarayya ta kama shi tare da mika shi zuwa Najeriya daga Kenya.
Da yake tabbatar da shirin Atikun, Darakta Janar na kungiyar yakin neman zaben Atiku/Okowa a jihar Anambra, Farfesa Obiora Okonkwo, ya ce dan takarar PDP zai dogara da hukuncin kotun daukaka kara na sakin mai fafutukar kafa kasar Biafra ne kawai.A cewar Okonkwo, kotun daukaka kara ta fito karara cewa Kanu ya kasance mai ‘yanci kuma babu wata kotu da za ta sake gurfanar da shi kan laifin da ake zarginsa da shi.
Jigon na PDP ya kuma bayyana cewa daya daga cikin muhimman shirye-shiryen Atiku shi ne ‘tabbatar da zaman lafiya na dindindin’ a sassan kasar nan musamman yankin Kudu maso Gabas, domin cimma hakan, ya ce Atiku zai saki dukkan masu tayar da kayar baya a yankin Kudu maso Gabas da ke tsare tare da tabbatar da an shawo kan rikicin yankin.
Don haka ya bukaci al’ummar yankin da su jajirce wajen ganin dan takarar jam’iyyar PDP ya lashe zaben da za a yi a ranar 25 ga watan Fabrairu, tare da sanin cewa yana da kyakkyawar manufa ga yankin nasu baki daya, domin duk zai sako mutanensu ba tare da beli ba.“Ina fadar haka ne da duk wani nauyi da Atiku zai baiwa Nnamdi Kanu ba tare da wani sharadi ba. Wannan yana cikin ajandar Atiku na samar da zaman lafiya na dindindin a yankin Kudu maso Gabas.
Bugu da kari, zai kuma yi amfani da hanyoyin siyasa don sakin duk wadanda ke tada kayar bayan IPOB na gaskiya da ake tsare da su ba tare da gurfanar da su a gaban kotu ba.Gwamnatin Atiku za ta yi tattaunawa sosai da kungiyar da sauran su, da nufin maido da imaninsu a kasar, tare da sanya su cikin kokarin inganta Najeriya.
Duk da haka, za a magance abubuwan da suka aikata laifuka da yanke hukunci.“Don haka abin da muke cewa shi ne ta faru, dole ne a zauna lafiya don zabe a Kudu maso Gabas, da kuma bukatar ‘yan Kudu maso Gabas su koma bayan PDP,” inji shi.Da wannan shiri, Atiku ya bayyana cewa shi ne dan takara daya tilo da ke da shirin tunkarar al’amuran yankin Kudu maso Gabas, domin amfanin yankin da kasa baki daya.
Tuni wannan alwashi na Atikun ya harzuka al’ummar Arewacin Najeriya wadanda ke ganin sakin Kanu rashin adalci ne ga al’ummar Arewa da Kanu ya tunzura yan bindigan IPOB suka kashe, da jami'an tsaro na kasa da sauran alummun wasu yankunan kasar.Wannan zance ya janyowa Atikun bakin jini a Arewa inda mutane ke cewa ya nunawa kurciya baka.