LABARI DA DUMI DUMI KALLI YADDA ABDULRA'UF MATAWALLE (SARKIN YAKIN BUHARI MAI MURABUS YAKE BAYYANA CEWA👇👇

Ba Mu Da Wata Hujja Da Zai Sa Mulki Ba Zai Koma Kudu Ba, Tunda Buhari Ya Yi Shekara Takwas

Daga Abdulra'uf Matawalle (Sarkin Yakin Buhari Mai Murabus)

...gani ga wane, ya isa wane tsoron Allah

Salon siyasar da makarraban shugaban kasa Buhari su dauko ta nuna ķýàmar su ga 'yan kudancin Nijeriya ba za ta haifar wa Nijeriya 'da mai ido ba.

Boko Haram da kidnapping ba su yi tasiri wajen raba Nijeriya ba amma wannan tsari na nuna ķýama ga ya'n kudu wallahi zai raba Nijeriya. 
Cijin gaggawa ina kira ga shugaban tsaro na farin kaya da su gaggauta shawo kan abun da cabals da shigaban Babban bankin Nijeriya suke kokari jefa kasar. Muddin ko ba a yi gaggawar rusa wannan tsirarun mutanen ba wato cabals to mufa ya'n Arewa da bàŕayin Gwamnati da suka kafa kamfanonin su a kudu da dukiyar su saidai fa su hakura don ba takaka kadai musifar za ta shafa ba har da manyan ya'n kasuwan mu na Arewa kamar su DANGOTE, BUA, AA,RANO, da dai sauran su.

Babu wata hujja ko dalili da zai sa ba za mu bar mulki ya koma kudu ba tunda dai Buhari ya yi takwas suma ya'n kudu su yi takwas.

Ba mu da komai a Arewa da ya rage mana noma, kuma shi ma 'yan garkuwa da mutane sun hana mu yi, ba mu da teku, ba mu da mai, ba mu da kamfanoni. A Arewa sai talauci da rashin tsaro.

Ina so na yi amfani da wannan kafa don jinjinawa gwamnonin APC  da suka je suka kai kukan talakawan su wajen Buhari. Allah ya saka masu da alkairi, sun nuna talaka ne a gabansu.
Previous Post Next Post