SOYAYYA GAMON JINI

SOYAYYA GAMON JINI 1

HIKAYAR ALISHARU DA YARINYA ZUMURRAZI

Majidu ƙasaitaccen attajiri ne a cikin Birnin  Hurassana. Yana da dukiya mai yawa, da bayi da kuyangi, farare da baƙaƙe. Sai da ya shekara sittin sa'annan Allah Mai Girma da Ɗaukaka ya nufe shi da ganin tsatsonsa, matarsa ta haifa masa ɗa namiji, ya sa masa suna Alisharu.

Yaro ya girma cikin kyakkyawar sura da fuska ma'abuciyar haske tamkar wata a daren cikarsa, ya tashi cikin ladabi da biyayya, ya san fannonin ilimi iri iri. Lokacin da ya isa mutum, sai mahaifinsa ya kwanta ciwon ajali. Da Majidu ya ga ciwonsa ba na tashi ba ne, sai ya kira ɗansa ya ce, "Ya ɗana, ina ganin ciwon nan nawa ba na tashi ba ne, ina so in yi maka wasiyya. Ka saurari abin da zan gaya maka da kunnen basira, idan ka yi amfani da shi ko bayan raina ba za ka tozarta ba."

Alisharu ya matso kusa ga mahaifinsa, hawaye na zuba daga idanunsa, ya ce, "Ya mahaifina, mecece wasiyyarka zuwa gare ni?"
Majidu ya ce, "Ya ɗana, ina horon ka da ka yi hankali da mutane, kada ka ba su amana. Ka guji aikata duk wani abu mara kyau. Kada ka yi tarayya da mutanen banza. Domin kuwa zama da mutumin banza, tamkar zama a maƙera ne, ko wutarta ba ta ƙona ka ba, hayaƙinta zai dame ka. Don haka ka zama mai dogaro da kanka, kada ka kuskura ka dogara ga wani. Wannan ita ce wasiyyata zuwa gare ka." Alisharu ya ce, "Na ji na ɗauka, ya mahaifina. Bayan wannan me kuma ya kamata in yi?"

"Ka zama mai kyautatawa ga kowa," mahaifinsa ya amsa masa, "kodayaushe ka kasance mai tausayi da jinƙai ga mutane. Ka yawaita alheri, domin shi alheri danƙo ne ba ya faɗuwa ƙasa banza."

"Na ji na karɓa, zan kuwa yi aiki da dukkan abin nan da ka gaya mini. Akwai sauran wani abu kuma da ya kamata in yi?"

Majidu ya ce, "Ka riƙa tuna Allah a kowane lokaci, shi ma sai ya tuna ka. Ka zama mai tattalin dukiyarka, kada ka yi almubazzaranci. Idan ka banzatar da dukiyarka, to kuwa za ka koma cizon hannu. Domin za ka zama mafi ƙasƙanci daga cikin mutane. Ka sani cewa, dukiya ita ce darajar ɗan Adam a wannan zamani, kamar yadda aka faɗa a cikin wannan waƙa: 

Dukiya in ta yi ƙarewa,
Abokaina ka watsewa.

Dukiya in ta yi juyowa,
Abokaina ka dawowa.

Aboki kan zamo maƙiyi,
In babu tudu na dafawa

Maƙiyinka ya zan abokinka,
In ga harka ta damawa.

"Sai kuma me?" Alisharu ya tambayi mahaifinsa.

"Ya ɗana," Majidu ya ce, "kada ka aikata aiki face ka nemi shawara daga waɗanda suka fi ka shekaru. Kada ka biye wa son zuciya wajen aikata kowane irin aiki. Ka zama mai tausayin na ƙasa gare ka, sai na samanka su ji tausayinka. Kada ka ci mutuncin kowa, duk wanda ya ci mutuncinka ka ƙyale shi da Allah. Kada ka sha giya, domin ita ce tushen afkawa cikin masifu duka. Takan kawar da hankalin mai hankali, ya aikata dukkan abin da zuciyarsa ta riya masa. Wannan ita ce wasiyyata zuwa gare ka, ka kiyaye da waɗannan abubuwa da na hore ka da su. Allah ya yi maka albarka." Daga nan sai ya yi wata doguwar shaƙuwa, ya suma.

Yayin da ya farfado sai ya nemi gafara daga Allah, ya yi kalmar shahada, ya ce ga garinku nan. Alisharu ya yi kuka don baƙin cikin mutuwar mahaifinsa, ya roƙar masa gafarar Allah Maɗaukakin Sarki. Mutane suka hallara, manyansu da ƙanana, aka yi masa jana'iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, aka rufe shi a cikin kabari. Aka sauke Alƙur'ani mai tsarki a wajen kabarin nan. Aka yi addu'o'i, sa'annan aka rubuta waɗannan baitoci bisa ga kabarin:

Ƙasa ce farkon ɗan Adam,
Daga nan aka yi maka rayuwa.

Ilimin kalmomi ka sani,
Ka furta zance mai yawa.

Yanzu ka mutu ka koma ƙasa,
Ka bar mu da tsantsar damuwa.

Alisharu ya zauna cikin tsananin damuwa da baƙin cikin mutuwar mahaifinsa, ba a daɗe ba kuma sai mahaifiyarsa ta mutu. Ya aikata mata tamkar yadda ya aikata wa mahaifinsa. Bayan an gama zaman makoki, sai ya ci gaba da zuwa kasuwa, ya buɗe rumfar mahaifinsa, yana saye yana sayarwa, bai kula da kowa ba, kamar dai yadda mahaifinsa ya yi masa wasiyya.

Alisharu bai gushe ba bisa ga wasiyyar mahaifinsa tsawon shekara guda. Ana nan sai ya yi abota da wasu samari 'yan iska, waɗanda ba su ganin kan kowa da gashi. Sannu a hankali ya riƙa biye wa shawarwarinsu, suka karkatar da shi daga ɗabi'u na ƙwarai. Da ma an ce, zama da maɗaukin kanwa shi ke sa farin kai. Sai ya soma kwankwaɗar giya dare da rana, ya riƙa cewa a cikin ransa, '"Dubi duk tarin dukiyar nan da mahaifina ya bar mini, shin idan ban more wa rayuwata ba na mutu, wa zan bar wa ita?"

Sai ya shiga cikin dukiya yana ta bundun-bundum, ya riƙa tara samari 'yan birni yana kashe musu gara suna kwasa a fayau. Yau da gobe ba ta bar kome ba, kafin a ce haka dukiya ta kare sarai. Ana tattalinta ma ya aka ƙare balle an banzatar. Alisharu ya shiga mawuyacin hali na talauci, dukkanin abokansa suka guje masa da suka ga abin hannunsa ya ƙare. Ya sayar da rumfarsa, da gonakin da mahaifinsa ya bar masa. Kai, ta kai ma sai da ya sayar da tufafinsa duka, in ban da na jikinsa bai rage kome ba. Daga nan sai ya shiga taitayinsa, wasiyyar mahaifinsa ta faɗo masa. Ya yi nadama, lokacin da nadamar ba ta da amfani.

Wata rana sai ya wayi gari ba ya da ko dirhami, kuma ba ya da abin da zai ci. Ya zauna tun wayewar gari har zuwa rana tsaka bai kai ko loma ɗaya ga bakinsa ba, sai ya ce a cikin ransa, "Bari na tafi wurin abokaina da na yi wa karimci, na san ba za a rasa ɗaya daga cikinsu wanda zai taimake ni da abin da zan ci ba.

Ya tashi ya riƙa bin gidajen abokaninsa ɗaya bayan ɗaya, amma duk wanda ya ƙwanƙwansa wa ƙofa, da ya leƙo ya ga shi ne, sai ya mayar da ƙyaure garam ya rufe, yana cewa, 'hala ni na ƙarar maka da dukiya da za ka dame ni da roƙo?' Haka ya yi ta ragaita tsakanin gidajen abokai har ya gaji, babu ɗaya daga cikinsu da ya ko baɗa masa ƙasa. Daga nan sai ya nufi kasuwa yana tunanin inda zai sami 'yar lomar da zai jefa wa hanjinsa da ke ta faman ƙugi a cikinsa. Da shigarsa kasuwa sai ya hangi mutane sun yi dafifi, sun zagaye wani abu a tsakiyarsu suna kallo. Sai ya ce a cikin ransa, "Shin me waɗannan mutane ke kallo ne, bari in matsa in ɗebe kwarkwatar ido."

To dika dika anan zamu dasa aya adakacemu domin kawo muku shiri nagaba mungode.
Previous Post Next Post